Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kalla Mutane Hudu Sun Mutu Sakamakon Wani Hadarin Jirgin Ruwa A Jihar Taraba

A Kalla Mutane Hudu Sun Mutu Sakamakon Wani Hadarin Jirgin Ruwa A Jihar Taraba
A Kalla Mutane Hudu Sun Mutu Sakamakon Wani Hadarin Jirgin Ruwa A Jihar Taraba

A kalla Mutane hudu sun mutu sakamakon wani hatsarin Jirgin ruwa a babban kogin Binuwai da ya ratsa karamar hukumar Ibbi dake Jihar Taraba. Jirgin mai daukar mutane ne da kuma motocinsu zuwa kasuwannin kauyukan da ke ci mako-mako a yankin na karamar hukumar Ibbi.

TARABA, NIGERIA - Abdulrazak Abubakar Maito sarkin barjin Ibbi kuma shugaban masu aiki da jiragen ruwa a kwatar Ibbi, ya ce yanzu haka dai an samo gawarwaki biyu, kuma suna neman sauran biyun a cikin kogin, sai dai ba su yi nasara ba tukunna.

Abubakar Aliyu kuma iyalansa su biyu ne suka rasu sakamakon wannan hastari na jirgin ruwa, kuma ya kara da cewa yanzu haka suna cikin tashin hankali sosai saboda aukuwar lamarin.

A Kalla Mutane Hudu Sun Mutu Sakamakon Wani Hadarin Jirgin Ruwa A Jihar Taraba
A Kalla Mutane Hudu Sun Mutu Sakamakon Wani Hadarin Jirgin Ruwa A Jihar Taraba

Shugaban karamar hukumar Ibbin Hon. Dr. Bala S. Bako ya tabbatar da faruwar hatsarin jirgin ruwan, ya kuma yi kira ga gwamnatin Jihar da ta tarayyya Nigeria da su kawo musu agajin gaggawa domin rayuwarsu na cikin hadari a yankin.

Yayin da muke hada wannan rahoton mun nemi jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba amma haka ba ta cimma ruwa ba.

Saurari rahoton Salisu Muhammad Garba:

A Kalla Mutane Hudu Sun Mutu Sakamakon Wani Hadarin Jirgin Ruwa A Jihar Taraba I.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG