Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taraba: Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Yara 7 Da Rushewar Gidaje Sama Da 200


Wata mummunar ambaliya
Wata mummunar ambaliya

Al’ummar Karamar Hukumar Gassol da ke jahar Taraba ta arewacin Najeriya na cikin matukar tashin hankali biyo bayan wata mummunar ambaliya wadda ta yi sanadin salwantar rayukan yara a kalla bakwai baya ga rushewar gidaje sama da dari biyu. Tuni wasu da dama da su ka rasa muhallansu su ka nemi mafaka a ginin makarantun gwamnati.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya zo da iska mai karfi mai gudun tsiya ne ya yi sanadin wannan rashe rahen rayuka da asarar dukiyoyi a garin Mutum Biyu. Hakazalika wasu da dama kuma sun samu raunuka.

Wani mutum mai suna Muhammad Sanusi Gambo, wanda ya shaidi al’amarin kuma ya na cikin wadanda su ka je makabarta yin jana’izar mamatan, ya ce a gaban idonsa aka bisne yara bakwai wadanda akasari gine gine ne su ka fada kansu. Ya ce guda bakwai din wadanda ma ya sani Kenan, banda wadanda su ka mutu a sassan garin. Ya ce gidaje dai dai ne a bayan gari da bas u rushe ba.

Mallam Hashim Musa, daya daga cikin iyayen da su ka rasa ‘ya’yansu sakamakon ambaliyar, ya ce bayan da ya ji kukan yaransa sai ya je ya yi ta kwaye bulo bulo ya samu daya dansa da rai ya zakulo shi; bayan da ya sake komawa, sai ya tarar da dayarsa ta mutu cikin baraguzan bulo, ya zakulo gawarta. Shi ma Alhaji Khalil Umar, daya daga cikin iyayen da su ka rasa ‘ya’yansu ya ce gini ne ya fadi kan dansa. Duk wani kokarin jin ta bakin Shugaban Karamar Hukumar ya ci tura.

Saurari cikakken rahoton Salisu Lado:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG