Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwashe kwanaki ana tafkawa a Yaounde babban birnin Kamaru, ya yi sanadin mutuwar wata yarinya da ruwa ya dauke a ranar 30 ga watan Yuni. Haka zalika a ranar Alhamis da ta gabata, ruwan ya haifar da ambaliya a wasu yankunan birnin, musamman a Municipal Roads da Avenue Kennedy.
A hirar ta da Muryar Amurka wata 'yar kasuwa mai suna Melanie ta ce “Ruwa ya cika hanya har ya hadiye motocin mutane. Nima ina da bidiyo da dama a waya ta inda ake ganin yadda ruwan yake barna”
Wata makobciyarta kuma tace ta samu dabarar labewa “Kadan ruwan sama ya fara sauka, sai inje in fake, kadan ya tsagaita sai in fito in ci gaba da kasuwanci na”.
Wani mutum da ya samu ya ketare hanya da kyar. Ya na mai cewa “Ruwa ya cike hanya kamar yadda kake gani. Karafunan jikin bango muke kamawa muna bin bango domin ketarawa zuwa wancan gefe. Abin ya fi karfinmu. Motoci da kake gani a can ruwa ya hadiye su. Yanzu haka yashi ya riga ya shiga injin motocin mu”.
Wannan shi ne kukan mazauna Yaounde a kowacce damuna. Gwamnati ta dau matakai da dama amma basu magance wannan matsalar ba. Duk da "sakamako mai gamsarwa" da aka samu na rage ambaliya a babban birnin a bisa hakon magudanar ruwa mai nisan kilomita 17 a kan kogunan da ke zuba a Yaounde da kewayen ta.
A watan Disamba na 2021, Bankin Raya Afirka (AfDB) ya bai wa Kamaru rancen sama da miliyan 38.55 na dalar Amurika a matsayin gudummawar ci gaban aikin.
Wannan aikin, wanda ya kamata a kammala shi a cikin watanni 48, bai kare ba har yanzu. Yana da nufin rage yawan ambaliyar ruwa a babban birnin kasar a cikin yanayin sauyin yanayi, tare da yin gyare-gyaren da ya dace don kare rayuwar mazauna birnin da muhallin su.
Saurari cikakken rahoton Mohamed Ladan cikin sauti: