NIGER, NIGERIA - Dama dai Jihar Nejan na daya daga jihohin Nigeria da Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya ta yi gargadin cewa za su gamu da ambaliyar ruwa a damana ta bana.
Wasu da Ambaliyar ta rutsa da su a garin na Kontagora sun ce sun tafka asara mai dimbin yawa, kuma a yanzu haka suna cikin wani hali mawuyaci na rashin muhalli kamar yadda wasunsu suka shaida wa Muryar Amurka.
Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Jihar Nejan, a tabakin shugaban hukumar, Alhaji Ibrahim Inga, ta ce har ya zuwa yammacin Alhamis ba su gama tantance yawan asara, da kuma ainihin yawan rayukan mutane da aka rasa ba.
Wannan dai yana zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar kula da yankunan samar da lantarki ta Najeriya HYPADEC ta fara aikin sake tsugunar da wasu garuruwa da a duk shekara suke samun ambaliya a jihar Nejan.
Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari: