Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta rika ba ma'aikatan kananan hukumomi guraben horaswa a cibiyar horas da sanin manufa da tsare-tasren kasar ko NIPSS a takaice domin inganta zamantakewar al'umma da rage tashin tashina.
Shugaban kungiyar Ibrahim Kahlil a ziyarar da suka kaiwa shugaban NIPSS, ya bayyana cewa ya gamsu da irin horon da cibiyar ke baiwa shugabanni shi yasa suke ganin shigar da ma'aikatan kananan hukumomi a tsarin horaswar zai taimaka gaya wajen samun saukin matsalolin da ake fuskanta a Najeriya. Kawo yanzu dai cibiyar bata daukan ma'aikatan kananan hukumomi. Idan an soma horas da ma'aikatan za'a samu bunkasar ayyukan kananan hukumomin da cigaban kasa. Idan an bar kananan hukumomi su tsaya da kafafunsu to za'a samu warakar matsaloli da yawa.
Shugaban cibiyar Farfasa Tijjani Bande yace zai gabatar da kukansu ga wadanda abun ya shafa. Amma yace cibiyar tana fitar da tsare-tsaren da zasu wanzar da zaman lafiya a kasar.
Ga rahoton Zainab Babaji.