Rundunar tace ta samu nasarar kwato yarinyar da aka sace daga wata makaranta a jihar ta Anambra dake kudu maso gabashin Najeriya. Rundunar kuma na cigaba da tsare budurwar da ta sace yarinyar.
Usman A Gwari kwamishanan 'yansandan jihar Anambra yayi karin haske akan yadda lamarin ya faru a hirar da yayi da wakilin Muryar Amurka Abubakar Lamido Sakkwato a ofishinsa.Yace wata mai shekara 13 ta sato wata 'yar shekara uku. Yarinyar 'yar shekara ukun tana makaranta tana wasa a waje da sauran 'yan yaran sai ita budurwar ta shiga harabar makarantar. Sai ta samu yarinyar tana wasa sai ta lallabeta ta fita da ita. Ta kaita gidansu ta zauna da ita har tsawon makonni biyar tana kokarin zata sayar da ita wa wasu da suka hada baki.
Ranar da mutanen zasu zo rundunar 'yansandan ta samu labarin inda yarinyar take. Nan take 'yansanda suka tafi suka kamata tare da duk wadanda suke cikin gidan. Mutumin da aka shirya dashi ya samo masu saye ana kan nemansa shi ma a kamashi.
Barauniyar budurwar tace tun da ta bar iyayenta bata da abun yi ko hanyar rayuwa sai wani ya bata shawara. Ya fada mata cewa akwai wasu da basu taba haihuwa ba kuma suna neman da ko diya ido rufe. Dalili ke nan da ta saci yarinyar. Tace wannan shi ne karon farko da ta shiga harkar sata da sayar da kananan yara. Amma tace tayi nadama yanzu.
Ga rahoton Abubakar Lamido Sakkwato.