Shugaban kungiyar Umar Abdullahi shi ya sanarda kokarin biyawa gwamnan kudin sake tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar. Yace ya zo wurin shugaban jam'iyyar na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Muazu akan suna neman izini su biya miliyan uku kudin yankar takardar zabe ma gwamnansu.
Da aka tambayeshi dalilin daukar matsayin yanzu tun da ba'a fara batun takara ba yace sun kawo ajiyar miliyan uku ne yanzu. Idan lokacin yayi kuma aka ce miliyan biyar ne sai su bayar da cikon.
Umar Abdullahi yace sun dauki matakin da saidai wasu jihohi su biyo bayansu domin ba'a samu jihar da manomanta suka zo suna neman gwamnansu ya sake tsayawa takara ba. Yace abubuwan da gwamnansu yayi masu suna da yawa. Yace kwanan nan yace akwai wata hadaka tsakanin gwamnatin Gombe da bankin Jais, wato bankin Musulunci inda zasu raba tallafin bashi na taki. Yanzu an kawo tiraktoci guda dari uku. Gwamnatin tana kuma taimakawa manoman rani da basu famfo da garmomi da sauransu.
Dangane da wai su tsaya a fitar da gwani sai shugaban yace wannan lamari ne na jam'iyyar PDP, amma su suna fadin ra'ayinsu ne. Kudinsu ne na manoma kuma a matsayin abun da yayi.
Yanzu dai zasu jira su ji sakamakon wasikar da suka bayar yayin da suna cigaba da rabon bashin takin da bankin Jais ya basu.
Ga karin bayani.