Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Halaka Mutane 52 A Harin Kunar Bakin Wake A Afghanistan

Mutane sun rude bayan harin kunar bakin wake kan 'yan Shi'a a Kabul.
Mutane sun rude bayan harin kunar bakin wake kan 'yan Shi'a a Kabul.

Jami’an kasar Afghanistan sun ce an kashe akalla mutane 52 da suka hada da mata da kanannan yara a harin kunar bakin waken da aka kai a wani wurin ibada na ‘yan Shi’a dake Kabul.

Jami’an kasar Afghanistan sun ce an kashe akalla mutane 52 da suka hada da mata da kanannan yara a harin kunar bakin waken da aka kai a wani wurin ibada na ‘yan Shi’a dake Kabul.

Jami’ai sun ce a kalla dan kunar bakin wake daya ya tarwatsa nakiya kusa da wurin Ibadan Abu Fazel, lokacinda masu ayyukan ibada suka taru yau Talata domin bukin Ashura. Sama da mutane dari kuma suka jikkata a harin.

Shaidu sun ce asibitai dake yankin sun cika da wadanda suka ji raunuka.

Hukumomi sun bayyana kyautata zaton cewa adadin wadanda harin ya rutsa da su zai karu.

A halin da ake ciki kuma, jami’ai sun ce wani harin da aka kai kan wani wurin ibada dake birnin Mazar-e-Sharif dake arewacin kasar ya kashe mutane hudu. Babu tabbacin ko an tunkari ‘Yan shi’a ne a harin na biyun.

Kungiyar Taliban ta bada sanarwa yau Talata ta bayyana cewa, bata da alhakin kai hare haren, da ta bayyana a matsayin rashin imani ta kuma dora a kan makiya.

Yau talata ake kammala bukukuwan Ashura da ake gudanarwa na tsawon kwanaki goma, wanda ya kasance hutu mafi muhimmanci ga musulmi ‘yan Shi’a, inda ake tunawa da mutuwar limami Hussein, jikan annabi Mohammadu mai tsira da aminci.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG