Yau Lahadi nan idan Allah ya yarda tsohon shugaban kasar Panama, Manuel Noriega wanda yayi mulkin kama karya ta soja a cikin shekaru alif dari tara da tamanin zai koma gida.
Tsohon shugaban ya share fiye da shekaru ashirin a gidajen wakafi anan Amirka da Faransa bayan da aka same shi da laifi bisa caje cajen safarar miyagun kwayoyi da bada sahun kudaden haram. Da sanyin safiyar yau Lahadi ya bara kasar Faransa a hannun hukumomi Panama.
Tsohon shugaba Manuel Noriega yana fuskantar hukuncin dauri shekaru ashirin a Panama a saboda laifuffukan da ya aikata a zamanin mulkinsa ciki harda kashe masu hamaiya dashi.
Shi dai Noriega wanda yanzu shekarunsa saba’in da bakwai a duniya, ya cancanci ayi masa daurin talala a saboda shekarunsa. Gwamnatin kasar Panama ce zata yanke wannan shawara.
Wasu masu zanga zangar sunyi gangamin kafin ya koma kasar, suna kira ga gwamnati data ci gaba da garkame shi a gidan yari.
Shi dai Noriega yaja ragamar mulkin Panama daga alif dari tara da tamanin da uku zuwa alif dari tara da tamanin da tara. Da shi jami’in hukumar leken asirin Amirka ta CIA ne, kafin suka bata da Amirka, sa’anan aka hambarar da gwamnatinsa bayan da Amirka ta mamaye Panama a alif dari tara da tamanin da tara