Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Kashe Mutane 73 A India


Masu aikin ceto suke amfani da igiyoyi wajen ceto mutane daga asibitin da gobara ta kama a Kolkata, a India.
Masu aikin ceto suke amfani da igiyoyi wajen ceto mutane daga asibitin da gobara ta kama a Kolkata, a India.

Gobara ta kashe fiyeda mutane 70 a wani asibiti mai zaman kansa a birnin Kolkata dake gabashin India.

Gobara ta kashe fiyeda mutane 70 a wani asibiti mai zaman kansa a birnin Kolkata dake gabashin India.

Hukumomi suka ce da sanyin safiyar yau ne gobarar ta cinye asibitin da ake kira AMRI a babban birnin jihar Bengal.

Tashoshin talabijin dake yankin suna nuna hotunan masu aiki dauke da marasa lafiya kan gadajen jigilar masu jinya, yayinda dangin marasa lafiya a asibitin suke tsaye a waje, yayinda hayaki ya murtuke ginin mai benaye.

Wani mataimakin shugaban asibitin yace, mutane 73 ne suka halaka a gobarar, cikinsu har da ma’aikatan asibitin su uku. Yace akwai marasa lafiya 160 a asibitin lokacinda gobarar ta tashi.

Wan nan ce gobara ta biyu a asibitin, cikin shekaru uku.

Babban ministan yammacin Bengal Mamata Banerjee, ta fara daukan matakan soke lasisin asibitin. Tayi alkwarin za a kaddamar da cikakken bincike kan wan nan lamari, bayan da jami’an gwanati suka yi zargin cewa wasun ma’aikatan asibitin sun gudu da barkewar gobarar.

Haka kuma tace hukumomi zasu dauki mataki idan aka samu matakan kashe gobara asibitin sun gaza mizanin da gwamnati ta tsaida.

Amma wani babban jami’in asibitin yace asibitin yabi dukkan sharadi kan gobara sau- da kafa. Yayi alkwarin asibitin zai biya diyya ga iyalan wadanda gobarar ta rutsa dasu.

‘Yan kwana-kwana sunyi bakin kokarinsu na shawko kan wutar, da kuma ceto wadanda gobarar tasa suka makale cikin ginin, bayan da suka kutsa ta cikin hanyoyin da ke unguwar, kamin su kai ga asibitin.

Jami’ai suka ce gobarar ta barke ne da ginin karkashin kasa na asibitin, inda ake adana sinadarai.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG