A yau Litinin, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa birnin Maiduguri, fadar gwamnatin Borno, domin jajantawa gwamnati da al'ummar jihar game da iftila'in ambaliyar ruwa ta baya-bayan nan.
Tinubu wanda ya isa birnin maiduguri da misalin karfe 3 da mintuna 40 na la'asar, nan da nan ya zarce zuwa daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira na wucin gadi domin jajantawa wadanda ambaliyar ta rutsa dasu.
A sansanin, Shugaba Tinubu ya baiwa 'yan gudun hijirar tabbacin samun tallafi daga gwamnatinsa.
An ruwaito Tinubu na cewa, "ina kara tabbatar muku cewa zamu taimakeku, zaku samu tallafi daga garemu. Allah yayi muku albarka."
Tawagar Shugaba Tinubun ta kunshi Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godwills Akpabio da Ministan Aikin Gona Abubakar Kyari da sauran masu taimakawa shugaban kasa.
Babban Sufetan 'Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya kasance a filin saukar jiragen saman sojojin dake Maiduguri domin tarbar shugaban kasar, kasancewar ya isa birnin tunda fari domin rangadin duba barnar da ambaliyar ta yiwa wasu gine-ginen 'yan sanda.
Dandalin Mu Tattauna