Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa: Wasu Mazauna Maiduguri Sun Ce Adadin Mutanen Da Suka Mutu Ya Haura 30


Wasu mazauna Maiduguri suna yin kaura bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanninsu (Hoto: Facebook/NEMA)
Wasu mazauna Maiduguri suna yin kaura bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanninsu (Hoto: Facebook/NEMA)

Wani mazaunin unguwar Costom, Maina Gana, ya tabbatar da ganin gawarwaki kimanin 28 a ruwa.

Adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta yi sanadin salwantar rayukansu a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya kai 65 in ji wasu da ambaliyan ruwan ta shafa.

Wannan alkaluma sun yi hannun riga da wadanda hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta fitar inda ta ce mutum 30 ne suka rasa rayukansu.

Duk da har yanzu ba a kai ga tantance irin asaran rayuka da dukiya da aka yi ba a dalilin ambaliyan ruwan, wasu anguwanni birnin na Maiduguri da ke kusa da juna sun tattara adadin wadanda suka rasa rayukansu inda suka tabbatar da mutuwar mutum 65.

Maina Gana wani mazaunin anguwan Costom ya tabbatar da ganin gawarwaki kimanin 28 a ruwa inda wasu anguwanni ma zuwa yanzu suka cire adadin wadanda suka rasa ransu, wanda ya ba da jimullar mutum 65.

Bayan ambaliyan ruwa da ta mamaye a birnin Maiduguri a daren Litinin wayewar garin Talata, har yanzu ruwa bai janye daga wasu sassan anguwanni da ambaliyar ta shafa ba.

Kimanin shekaru 30 kenan da irin wannan ambaliya ta auku a birnin Maiduguri, sai dai ambaliyar bana ta fi ta wancen lokacin, inda a wannan karon ta ci wurare da dama.

NEMA ta ce mutum sama da 400,000 ambaliyar ruwan ta raba da muhallansu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG