Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NEMA A Najeriya Ta Ce Ba Ta San Adadin Wadanda Suka Rasa Ransu A Ambaliyar Ruwan Garin Maiduguri Ba


Ambaliyar ruwa a Maiduguri
Ambaliyar ruwa a Maiduguri

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta bayyana cewa har yanzu ba a kai ga tantance yawan rayukan da aka yi asara ba, a dalilin ambaliyar ruwan da ta faru a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Tun bayan bayyanar adadin mutane 30 da suka mutu da hukumar ta NEMA ta sanar, sanadin ambaliyar ruwan da aka yi a Maiduguri, daga bisani hukumar ta bayyana cewa, a yanzu ba ta da takamaiman adadin wadanda suka rasa rayukansu, saboda har yanzu ruwa bai janye daga unguwanni da dama da ruwan ya cinye ba.

Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA, Malam Sirajo Abdallah ne ya bayyana hakan, inda ya ce baya ga mamaye unguwanni da ruwan yayi, akwai sauran wurare kamar makabartu da sauransu da ruwan ya mamaye.

Ya kuma ce dole ne sai idan ruwan ya janye sannan a iya tantancewa a kuma gano irin barnar da ruwan yayi, kuma za a gudanar da tantancewar tare da shugabannin al'umma a, unguwanni dabam dabam da ruwan ya ci.

Ambaliyar ruwan ta Maiduguri dai ta raba mutane da dama da matsugunnansu, inda gidaje da dama suka rushe, wasu kuma ruwa ya shafe su baki daya.

A yanzu dai gwamnatin jihar Borno ta tsugunnar da dubban mutanen da ambaliyar ta raba da gidajensu a sansanonin 'yan gudun hijira, sai dai mutane da dama sun koka da rashin abinci da wajen kwanciya, inda suka bayyana cewa a wasu lokutan ana dukansu akan layin karbar abinci, ba babba ba yaro, lamarin da suka ce ya kai ga rasa rai, wasu kuma na kwance a asibiti sakamakon kuna da su ka samu a wurin karbar abinci.

Hukumomi da masu hannu da shuni cikin al’umma, manya da kananan 'yan kasuwa a Najeriya na ci gaba da aikewa da gudummuwa domin tallafa wa al’ummar ta Maiduguri da ambaliyar ruwan ta shafa.

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG