Uwargidan Shugaban Najeriya, Remi Tinubu ta mika sakon jajenta ga al’umar jihar Borno bisa ibtila’in ambaliyar ruwa da ya afkawa birnin Maiduguri a farkon makon nan.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafukan sada zumunta uwargidan shugaban kasar ta ce, “zuciyata da addu'o'ina na tare da ku a cikin wannan mawuyacin lokaci. Rashin rayuka, gidaje, da hanyoyin rayuwa babban nauyi ne da babu wata al’umma da ya kamata ta fuskanta.”
“Ina jajantawa Gwamnan Jihar Borno, Mai Girma Farfesa Babagana Umaru Zulum, matarsa, da dukkan al’ummar jihar a yayin da suke fuskantar mummunan tasirin ambaliyar ruwa da ta faru a kwanan nan.” Ta kara da cewa.
“Ina rokon Allah ya taimaki jihar Borno ta fita daga wannan masifa ta zama mai karfi da juriya.” In ji Remi.
Akalla mutum 30 ya zuwa yanzu hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta ce sun mutu yayin da dubban daruruwa suka rasa muhallansu.
Wasu mazauna birnin sun ce adadin ya haura haka.
Ana dai fargabar adadin mace-macen zai fi hakan saboda har yanzu ruwan bai kammala janye wa ba ta yadda zai ba da damar gudanar da ayyukan ceto.
Ambaliyar ta samo asali ne bayan da madatsar ruwan Alau ta fashe a daren Litinin wayewar garin Talata.
Dandalin Mu Tattauna