Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UAE Ta Bada Gudunmowar Kayan Agaji Ga Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Najeriya


NIGERIA-FLOOD
NIGERIA-FLOOD

A cewar NEMA, jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa a Najeriya, Salem Alshamsi, ne ya mika kayan agajin ga hukumomin Najeriya a filin saukar jiragen saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Hadaddiyar Daular Larabawa ta bada gudunmowar “tan 50 na kayan agaji” ga gwamnatin tarayyar Najeriya domin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwan baya-bayan nan ta shafa.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta sanar da hakan a sanarwar da ta fitar a jiya Lahadi.

A ranar 10 ga watan Satumbar da muke ciki ne, dubban mazauna unguwannin Fori da Galtimari da Gwange da Bulabulin na birnin Maiduguri suka kauracewa gidajensu sakamakon ambaliyar ruwan data afkawa yankin.

Ambaliyar ta afku ne sakamakon fashewar da madatsar ruwa ta Alau ta yi wacce ta shafe tsawon mako guda a cike da ruwa.

A cewar NEMA, jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa a Najeriya, Salem Alshamsi, ne ya mika kayan agajin ga hukumomin Najeriya a filin saukar jiragen saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Manyan jami’ai daga hukumar NEMA da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya dana ofishin mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro ne suka karbi kayan agajin a madadin mutanen da ambaliyar ta shafa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG