Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwar Karu Ta Kone Kurmus


Gobara a kasuwar Karu
Gobara a kasuwar Karu

Wata mummunar gobarar da ta auku a kasuwar Karu da ke Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa ta yi sanadin janyo asarar dukiya mai yawa.

Wannan kasuwa tana kusa da mahadar Abuja da jihar Nasarawa, kuma ana samu masu zuwa cin kasuwar daga Abuja kullum.

Ya zuwa yanzu kasuwar ta kone kurmus da dukkan kayayyakin da ke cikin ta, wanda ba’a iya kayyade kudin su ba.

'Yan kasuwar da suka tafka asara sun shiga cikin halin dimuwa da kaduwa sosai.

Hukumar Kashe Gobara ta Abuja da ke da tasha a kasuwar ta fitar da sanarwa cewa ta fuskanci kalubale wajen isa cikin kasuwar, domin babu hanya saboda cunkoson kayayyaki da mutane da ke kokarin fita daga kasuwar, shi ya sa ba ta iya kashe wutar da wuri ba.

Hukumar ta ce sai da ta fasa wata Katanga sannan ta iya zura bututun ruwa da aka yi kokarin kashe wutar da shi, amma duk da haka kasuwar ta kone kurmus.

Gobarar ta fara ne da misalin karfe 7 na yamma, bayan mutane da dama sun rufe shagunan su, wasu kuma suna kokarin fita daga kasuwar.

Hukumar Kashe Gobara ta ce ba’a san musabbabin wutar ba amma tana ganin kamar tangardar lantarki ne ya jawo gobarar.

Hukumar ta kara da cewa ba’a rasa rayuka ba, amma an samu lalacewar kayayyaki da aka kiyasta sun kai na miliyoyin Naira.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG