Gobarar ta tashi ne a wata masana'anta da ke karkashin masana'antar batir na Aricell a Hwaseong, wani rukunin masana'antu da ke kudu maso yammacin Seoul babban birnin kasar. Amma daga ƙarshe an kashe wutar gaba daya.
Ma'aikata 18 na kasar Sin da kuma ‘dan kasar Lao daya na cikin wadanda suka mutu.
Har yanzu ba a tabbatar da asalin ma’aikaciyar da ta mutu ba, kamar yadda jami’in kashe gobara Kim Jin-young ya shaida wa manema labarai.
Kim ya ce gobarar ta tashi ne da karfe 10:31 na safe (0131 GMT) bayan da wasu nau'ikan batir suka fashe a cikin wani dakin ajiyar kaya dauke da batir guda 35,000, in ji Kim, inda ya kara da yace ba a san abin da ya haddasa fashewar ba.
Wani ‘dan jaridar Reuters ya ga ma'aikatan kashe gobara sun kwashe gawarwaki shida daga cikin masana'antar. Saboda tsananin gobarar, masu aikin ceto sun samu wahalar gano wadanda suka mutu, in ji Kim.
Shugaban kasar Yoon Suk Yeol ya ziyarci wurin da hatsarin ya afku daga baya a ranar Litinin. Ministan cikin gida Lee Sang-min ya yi kira ga hukumomin yankin da su dauki matakin hana duk wani sinadari mai hatsarin gurbata muhallin da ke kewaye.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna