Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashewar Tankar Mai Ta Hallaka Mutane 3 A Jihar Ribas


FILE PHOTO
FILE PHOTO

Al’amarin daya afku da misalin karfe 9 da rabi na safiya ya hada da wata tanka da ake zargin tana dauke ne da iskar gas wacce ta latse wata karamar mota tare da tarwatsewa a yayin da take kokarin shiga shatale-tale.

Mutane 3 sun hallaka sakamakon fashewar tankar mai a gadar Saman Obiri zuwa Ikwerre dake kan hanyar gabas zuwa yamma ta birnin Fatakwal, fadar gwamnatin jihar Rivers a yau Talata.

Al’amarin daya afku da misalin karfe 9 da rabi na safiya ya hada da wata tanka da ake zargin tana dauke ne da iskar gas wacce ta latse wata karamar mota tare da tarwatsewa a yayin da take kokarin shiga shatale-tale.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin a wata hirar wayar tarho, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, tace wadanda al’amarin ya rutsa dasu sun kone kurmus sa’ilin da tankar ta afka kan motar da suke tafiya a ciki.

An ruwaito ta tana cewar, “ina tabbatar da cewar mutane 2 sun mutu a gobarar tankar. Ni da kwamishinan ‘yan sandan jihar muna wurin da al’amarin ya faru a halin yanzu.”

“An yi nasarar kashe gobarar saidai har yanzu wurin nada hatsari saboda da gas din dake yoyo. don haka muke kira da masu ababen hawa dasu bi wasu hanyoyin ddomin kaucewa shiga hatsari.”

A yayin hada wannan rahoto, jami’an kashe gobara sun shawo kan wutar a yayin da dandazon jama’a suka taru domin kallo cikin tsauraran matakan tsaro.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG