Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Lalata Fiye Da Shaguna 180 A Babbar Kasuwar Sokoto


Kasuwar sokoto
Kasuwar sokoto

Fiye da shaguna 180 ne suka kone sakamakon gobarar data tashi a babbar kasuwar Sokoto da sanyin safiyar yau Litinin.

WASHINGTON DC - Rahotanni sun bayyana cewar, gobarar wacce ta taso daga daya daga cikin wuraren tara shara a kasuwar, ta bazu zuwa shaguna harma ta lakume wasu babura da aka ajiye a kusa da wurin.

A cewar Shugaban Kungiyar Masu Sana'ar Sayarda Babura a kasuwar, Muhammad Garba, gobarar ta sabbaba asarar dimbin dukiya, kasancewar abokan sana'arsu sun yi asarar dukiya ta biliyoyin nairori data hada da babura da kekuna dama kayan gyaransu.

Kasuwar Sokoto
Kasuwar Sokoto

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Sokoto data gaggauta daukar matakin tantance irin barnar da gobarar ta yi, tare da lalubo hanyoyin ragewa 'yan kasuwar da abin ya sha radadin asarar da suka tafka sakamakon gobarar.

Kasuwar Sokoto
Kasuwar Sokoto
Kasuwar Sokoto
Kasuwar Sokoto

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG