Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Asarar Dukiya Ta Miliyoyin Naira, Sakamakon Gobarar Data Tashi A Kasuwar Idumota Ta Birnin Legas


Kasuwar Idumota
Kasuwar Idumota

Wata gobara data tashi da a yau Laraba, a shagunan dake bangarorin nnamdi azikiwe da dacemo na kasuwar idumota ta jihar Legas, ta lalata dukiya ta miliyoyin nairori.

WASHINGTON DC - Gobarar ta shafi wasu gine-gine guda 3 ne, ciki harda wasu benaye masu hawa bibiyu da wani bene mai hawa daya, a bangaren kasuwar daya fi shahara da kasuwancin tufafi da takalma da jakunkuna.

Tuni dai jami'an hukumar kwana-kwana da bada agajin gaggawa ta jihar Legas da sauran hukumomin bada agaji suka isa wurin da al'amarin ya faru inda suka kaddamar da aikin kashe gobarar.

Kasuwar Idumota
Kasuwar Idumota

A cewar Shugabar Hukumar Kwana-Kwana ta jihar Legas, Margaret Adeseye, cibiyoyin kashe gobara na unguwannin Ebute Elefun da Ilupeju da Alausa sun tura jami'ai da kayan aiki domin taimakawa wajen shawo kan gobarar wacce tuni aka kaddamar da yaki da ita.

Har yanzu dai ba'a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba, amma an kaddamar da bincike akan hakan. Haka kuma, ba'a kai ga tantance asarar rai ko jikkata ba

Kasuwar Idumota
Kasuwar Idumota

Adeseye ta bukaci mazauna yankin su baiwa jami'an bada agajin gaggawa hadin kai tare da kaucewa wurin domin kiyaye lafiyarsu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG