Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaman Dardar Tsakanin Fulani Makiyaya Da Manoma A Kudancin Ghana


Nomadic Fulani and his cows
Nomadic Fulani and his cows

Yayin da Fulani ke kan yanyarsu ta kaura zuwa kudancin Ghana saboda dabbobinsu su samu abinci, wasu al'ummomin kudancin kasar na adawa da hakan kan dalilin cewa wai Fulanin na aikata wasu manyan laifuka, zargin da Fulanin su ka karyata.

Ana zaman dardar tsakanin Fulani makiyaya da al'ummar karkara ta Ejura da ke kudancin kasar Ghana sakamakon matakin da majalisar karkarar ala'adan Ejura ta dauka na bai wa fulani makiyaya wa'adin ficewa garin tare da haramta ma makiyaya da ke shiga garin da shanunsu alokacin rani. Abinda ke barazana ga tsaron kasar inji masharhanta.

Sarkin Ejura da ke jahar Ashanti, Barima Osei Hwedie, ya yi korafin cewa bayanan sirri da suka tattaro daga hukumomin tsaro ya tabbatar da cewa Fulani makiyayan shanu ne ke aiwatar da muggan laifuka ayankin da suka hada da garkuwa da mutana da fashi da makamai da fyade tare da lalata amfanin gonaki abinda yace:

" Mun bai wa Fulani makiyaya da suka shigo yankinmu wa'adin sati daya da su fice kazalika wadanda ke kan hanya daga jihohin arewa da kada su kuskura su zo saboda a shirye muke mu dau mataki akansu"

Sai dai ya kara da cewa "ba wai muna kyamar 'yan kabilar Fulani ba ne muna bukatar da alummarmu ita ma ta samu walwala."

Sakatarin kungiyar kabilar Fulani ta kasa da kasa wato Tabital Pilaku, Musah Yakubu Barry, ya fada wa Muryar Amurka a gefen wani taron kungiyar cewa wannan mataki ya haifar da matsala babba tare da bukatar da kungiyar kasa da kasa mai fafutukar raya cigaban Afurka Ta Yamma ta Ecowas tare da shugaban kasa Nana Addo su tsoma baki domin ganin an cimma daidaituwa saboda:

"wannan umurnin ya fito a makare kuma makiyaya na kan hanyarsu ta shigowa garin Ejura. Matsalar da za a fusanta muddan an hana su ta fi da abar su shigo. Wannan gari suke zuwa a duk lokacin rani fiye da shekaru goma kenan. Yanzu haka sun kusa shiga; in aka tare su, za su bazu su shiga gona su shiga ruwa yi barna sosai. A don haka muke bukatar da a dauki matakin fahimtar juna."

Umar Sanda Ahmad mai sharhi bisa harkar tsaro ya bayyana cewa hana shanu shiga garin Ejura awannan lokacinda dabbobin ke kwarara zuwa kudancin kasar domin kiwo ya haifarda matsala babba.Umar Sanda ya kara da cewa in akwai wani kuskure da sukeyi ya kamata ayi zama da su maimakon adauki wannan matakin ba'a sani ba sabo akansu.

Hon Bawa Muhammad Braimah mamba akwamitin tsaron ciki da wajen Ghana ta majalisar dattawan kasar ya bayyana cewa kwamiti dinsu ya isa Burkina Faso da Tarayyar Najeriya da Senegal a inda ya duba hanyoyin da ake bi domin cimma daidaituwa tsakanin manoma da makiyayan shanu. "Abin da muka gano shine akwai wasu manya manyan burtalin garken shanu da ake kafawa. A duk lokacin da makiyayi ya shigo sai shanunsa su yi kiwo a ciki." Gwamnati ta fara wasu a yankin Afram Plains a kasar amma kamata yayi da a inganta su. Ya jadadda cewa Fulani makiyaya ba su duka ne gurbatattu ba.

Halin yanzu Fulani makiyaya na kan hanyarsu da dabbobinsu zuwa kudancin Ghana. ko ya wannan al'amari zai kasance muddan sun shigo? Lokaci ne zai nuna.

Saurari cikakken rahoton Hamza Adams:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG