Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasafin Kudin 2023 A Ghana: Zamu Rage Shigo Da Kaya Daga Waje-Ministan Kudi Ofori Atta


Ministan Kudi a Ghana, Ken-Ofori-Atta
Ministan Kudi a Ghana, Ken-Ofori-Atta

Gwamnatin kasar Ghana ta bayyana wasu shirye shirye da zummar bunkasa samar da kayayyaki a cikin kasar a kasafin kudin shekarar 2023.

Ana sa ran wannan mataki dake kunshe a cikin ajandar gwamnati mai gimshikai bakwai domin farfado da tattalin arziki, zai taimaka wurin rage shiga da kayyaki daga kasashen waje da kuma irin mummunan tasiri da hakan ke da shi a kan darajar kudin kasar.

Da yake gabatar da kasafin kudin gwamnati na shekarar 2023, ministan kudi, Ken Ofori Atta, a bangaren bunkasa yin kayayyaki a cikin gida, a cikin abubuwa da dama da gwamnati ke niyar yi, zata rage kayayyakin da take sayowa daga kasar waje da ma abinci da kashi 50 cikin dari.

Ya ce gwamnati za ta hada kai da hukumar binciken kudi ta Ghana da hukumar binciken kudaden hukumomi cikin gida don tabbatar da bin ka’ida a wannan fanni.

Ya kuma bayyana cewa, gwamnati za ta goyi bayan shirin samar da sabbin dabarun musayar kayyyaki, ciki har da abubuwa da shugaban kasa ya bayyana a jawabinsa baya da ya yi wa al’ummar kasar.

"Za mu kuma tallafa wa manyan ayyukan noma da harkokin noma ta Bankin Bunkasa Ayyuka na Ghana," in ji ministan.

Ministan Kudi ya kuma yi nuni da cewa gwamnati za ta bullo da tsare-tsare na kariya da kuma kirkiro da sabbin masana'antun cikin gida.

Wannan shi ne zai ba su damar yin kayayyaki a nan da zasu suyi gogayya da kayan da ake shigowa dasu daga kasashen waje.

Mr. Ofori Atta ya bayyana wasu shirye shiryen gwamnati na habbaka aikewa da kaya zuwa waje.

Ya ce shirye shiryen sun hada da karfafa gwiwar amfani da kayyyakin da ake yi a cikin gida, kamar shinkafa ‘yar gida, da kaji da man girki da lemo da kan gini da sauransu.

“Mai girma Kakakin majalisa, kamar yadda na riga na nuna, dogaro mai yawa da Ghana ke yi kan shigo da kaya yana sanya matsin lamba ga Cedi, yana kuma haifar da ma'auni mara kyau na biyan kudi."

“A kalla, lissafin shigo da kaya a Ghana ya haura dalar Amurka biliyan 10 a duk shekara kuma ana lissafinsu da abubuwa daban-daban da suka hada da karfe, farin karfe, sukari, shinkafa, kifi, kaji, man girki, siminti, taki, magunguna, takarda tsaftace jiki (T’ Roll), karar tsakace, lemon ‘ya’yan itace da sauransu,” inji shi."

Ya ce a halin yanzu kasar na da karfin samar da kayayyaki a cikin gida wanda ya kai kusan kashi 45 cikin 100 na darajar kayayyakin da muke shigo da su duk shekara.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG