Mataimakin shugaban Ghana Dakta Mahmud Bawumia ne ya bayyana hakan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkar makamashi a Ghana, inda yake cewa "bayan tallafin asusun lamuni na IMF, ya kamata kasar ta nemi wasu hanyoyi da zata magance matsalolinta. Idan tsarin ya fara aiki, zai rage abin da ake kashewa, sannan zai rage ci gaban faduwar darajar kudin kasar da ake alakantawa da tashin farashin mai, a cewarsa.
Shugaban babban bankin kasar na Bank Of Ghana Dakta Ernest Addison, ya fada wa manema labarai bayan tsokacin mataimakin shugaban cewa manya-manyan kamfanonin hakar ma'adinai a Ghana na fitar da gwal da ya kai dalar Amurka biliyan uku a kowace shekara, don haka gwamnati zata rinka sayen kashi ashirin cikin dari na gwal daga garesu daga shekara mai zuwa.
Mai sharhi kan harkar makamashi a Ghana, kuma malami a jami'ar kimiyya da fasaha ta KNUST da ke Kumasi Dakta Kwame, yace wannan mataki ya taimaka musamman a wannan lokaci da kasar ke fama da tsadar man fetur, amma kuma matakin ba zai dawwama ba.
Dakta Kwame Sarkodie na ganin kamata yayi gwamnati ta maida hankali wajen farfadoda da babbar matatar mai ta kasa wato Tema Oil refinery, abinda yace hakan zai sa Ghana dogaro da kai wajen amfani da man fetir saboda kasar na hakar danyen mai cikin gida.
Shi kuwa mai sharhi kan harkar hakar ma'adinai ta kasa wato Baba Muhammad na ganin wannan mataki da gwamnati ta dauka yayi daidai tare da bai wa gwamnati shawarar cewa tayi kokarin farfado da matatar mai ta kasa ko da rance zata karba maimakon ta dukufa kan musayar man fetur da gwal.
Ana dai sa ran cewa tsarin zai fara aiki a karshen watanni uku na farkon shekarar 2023.
Saurari rahoton Hamza Adam: