Wuni guda bayan mummunan gobarar da ta tashi a gundumar Bronx a birnin New York da ke Amurka, hukumomi sun ce mutum 17 suka mutu a cikin wannan gobara ba 19 ba kamar yadda alkalumman fari suka bayyana.
Wannan adadi da hukumomin suka fitar ya biyo bayan zagawa da hukumomin suka yi a asibitoci da aka kai wadanda gobara ta rutsa da su, kamar yadda babban kwamishinan hukumar kwana-kwana ta birnin New York Daniel Nigro ya fadawa manema labarai inda ya kara da cewa injin din dumama daki ne ya yi sanadiyar gobara.
Asibitotci a birnin New York suna nan suna aiki gadan-gadan domin ceto gomman mutane da suke cikin hali na mutu-kwakwai-rai-kwakwai da suka shaki hayaki da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 17.
Ba a riga dai an bayyana sunaye mutanen da suka mutu ba, amma hukumomi sun ce yaran da suka mutu sun hada da mai shekaru 4 da mai 5 da mai 6 da yaran mata biyu masu shekar sha daya-daya da kuma wani yaro mai shekara 12 kana akwai daya da ba a kammala tantancesa ba.
Kimanin jami’an kashe gobara 200 ne suka yi kokarin kawar da wutar da ta tashi a hawa na uku a cikin bene mai hawa 19 dake unguwar Tremont a Bronx da hantsin ranar Lahadi.
Shugaban hukumar Kwana kwana a birnin New York ya ce hayaki da ya turnuke a cikin ginin ne ya yi sanadiyar mutuwar mutanen.
Nigro ya ce an kai gawarwakin asibitoci bakwai na birnin wanda ya yi bayani a kan sauya adadin wadanda suka mutu daga 19 zuwa 17 saboda an kirga wasu sau biyu biyu.
Kididdiga ta nuna cewa, kimanin mutum 44 ne suka ji rauni, amma 13 a ciki raunin nasu sun yi tsanani, lamarin da ka iya sanadiyar mutuwar su.