CDC ta ce mutumin matafiyi ne da ya dawo Amurka daga Afirka ta Kudu a ranar 22 ga Nuwamba. “Mutumin, wanda ya riga yayi cikakken allurar rigakafin cutar yanzu haka ya killace kanshi.
Wannan lamarin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Biden ke shirin sanya tsauraran sharuddan gwaji ga duk matafiya na kasa da kasa da za su shigo Amurka a wani bangare na kokarin dakile yaduwar sabon nau'in omicron na coronavirus.
Kafofin yada labarai sun ce gwamnatin za ta kuma bukaci duk wanda zai shiga Amurka ya yi gwajin COVID-19 kwana daya kafin ya kama hanyar zuwa, ba tare da la’akari da matsayinsa na ko sun yi allurar rigakafin ba.
Jami'ai sun kuma tattauna kan ko za a sanya wata bukata ga duk matafiya su keɓe kansu na tsawon kwanaki bakwai bayan isowarsu, da kuma duk matafiya da za su sake gwadawa cikin kwanaki uku zuwa biyar bayan shiga Amurka. Dokokin da aka tsara za su kuma shafi dukkan 'yan asalin Amurka da ke dawowa Amurka daga balaguron ketare.