Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hauhawar Omicron Ya Sa Asibitocin Amurka Jinkirta Tiyata


Asibitoci a duk faɗin Amurka suna jinkirin aikin fida na tiyata don samar da isassun ma'aikata da gadaje saboda hauhawar cutar COVID-19 nau’in Omicron dake yaduwa.

Mahukunta sun ce karancin ma’aikatan asibiti ya karu a cikin watan da ya gabata saboda yadda kwararrun likitocin ke kebance kansu saboda sun kamu da cutar ko kuma sun kusanci kwayoyin cutar.

Asibitoci a kusan rabin jihohin Amurka da suka hada da Maryland, Virginia da Ohio sun sanar da cewa za su dage aikin fida, kamar yadda wani nazari da kamfanin dillancin labarai na Reuters da wasu kafofin watsa labarai suka gudanar ya nuna. Su ma gwamnatocin jihohin New York, Illinois, da Massachusetts, duk sun aiwatar ko kuma sun ba da shawarar jinkiri irin wadanan aiyukkan fidan a jihohinsu.

Yawancin wuraren da asibitoci ke dakatar da aikin tiyata sun ga tashin ko karuwar yawan mutanen dake kamuwa da cutar COVID19 a wattanin Disamba ko Janairu, a bisa bayann da aka samu daga Cibiyoyin Kula da Cututtuka da Kariya: https://covid.cdc.gov/covid-data-tracker/#new-hospital-admissions show.

Haka kuma kampanin dillacin labaran reuters ya ruwaito cewa karin yaduwar Omicron ya kuma tilasta wa Cibiyoyin Lafiya na kasa da su jinkirta gudanar da aiyukkan tiyata a babban asibiti mafi girma a Amurka mai gudanarda binciken cututtukka. https://www.reuters.com/business/healthcare-pharmaceuticals/exclusive-us-nih-research-hospital-delays-elective-surgeries-omicron-wave-hits-2021-12-29

Dakatar da zaɓabbiyar tiyata na iya haifar da koma baya, da asarar miliyoyin daloli ga kudaden shiga ga asibitoci, kuma a wasu lokuta ya kan zama sanadin rashin lafiya ko mutuwa.

Kulawar musamman ga marasa lafiya na iya kasancewa mai mahimmanci, in ji Cynthia Cox, mataimakiyar shugaba a Cibiyar Kula da Iyali ta Kaiser. Dubun dubatar mutane fiye da yadda aka saba gani ne suka mutu daga cututtukkan da ba na COVID ba, a lokacin bazuwarta, kuma an yi imanin wasu daga cikin mace-macen suna da alaƙa da jinkirin samarda kulawa, in ji ta.

-Reuters

XS
SM
MD
LG