Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WHO: Adadin Masu Kamuwa Da Cutar COVID-19 A Duniya Ya Karu Da Kashi 11


COVID-19
COVID-19

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a duniya ya karu da kashi 11 cikin 100 a makon da ya gabata idan aka kwatanta da satin da ya wuce, inda nahiyoyin Amurka ne aka fi samun karin. 

Wannan na faruwa ne biyo bayan karin adadin a hankali da aka samu tun daga watan Oktoba.

A rahotonta na mako-mako da aka fidda ranar Talata da dare, hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu kusan mutun miliyan 4.99 da suka kamu da cutar afadin duniya daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Disamba.

Kasashen Turai ke da fiye da rabin jimlar, inda suka samu mutun miliyan 2.84 da suka kamu da cutar, ko da yake adadin ya zarta na makon da ya gabata ne da kashi 3 cikin 100 kacal. Haka kuma yankin ya fi ko wanne samun yaduwar cutar, inda ake samun mutun 304.6 cikin 100,000 dake kamuwa da cutar.

Hukumar WHO ta ce sabbin kamun cutar a nahiyoyin Amurka sun karu da kashi 39 cikin 100 zuwa kusan miliyan 1.48, kuma yankin shine na biyu wajen bazuwar cutar inda ake samun mutun 144.4 cikin 100,000 dake kamuwa da cutar. Amurka kadai an samu sabbin kamun cutar mutun fiye da miliyan 1.18, karin kashi 34 cikin 100 kenan.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu karin masu kamuwa da cutar da kashi 7 cikin 100 zuwa kusan 275,000 a Afirka.

Hukumar ta ce har yanzu akwai haɗari sosai a tattare da sabon nau’in omicron." Ta ambaci hujjoji da suka nuna cewa nau’in na habbaka fiye da na Delta, wanda har yanzu shi ya fi yawa a sassan duniya.

Hukumar ta fadi cewa an samu raguwar masu kamuwa da cutar a Afirka ta Kudu, kuma bayanan farko daga ƙasar, da Burtaniya, da Denmark sun nuna cewa an samu raguwar haɗarin kwanciya asibiti sanadiyyar omicron. Amma ta ce ana buƙatar ƙarin bayanai don fahimtar tsananin nau’in cutar, ciki har da amfani da iskar oxygen, da na’urar taimakawa numfashi da kuma mutuwa, bayan haka da yadda riga kafin COVID-19 ka iya yin tasiri kan nau’in cutar.

Hukumar WHO ta ce adadin wadanda suka mutu a fadin duniya da aka sanar a makon da ya gabata ya ragu da kashi 4 cikin 100 zuwa 44,680.

-AP

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG