Majalisar dattawa ta zartar da kudirin PIB zuwa doka ne bayan dogon nazari kan duk shawarwarin da rahoton kwamitin hadin gwiwa na bangaren hako albarkatun man fetur da bangaren sarrafawa na majalisar dattawa da ta wakilai da kuma iskar gas a kan kudurin na PIB.
Haka kuma majalisar dattawan ta amince da ba ‘yan kasuwa damar saka mafi yawan hannayen jari a kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC da kuma soke asusun daidaita farashin man fetur wato PEF da hukumar kayyade farashin albarkatun man fetur wato PPPRA.
Majalisar ta kuma amince da tsarin ba kamfanin NNPC kaso 30 cikin 100 na ribar da ake samu daga cinikin mai da iskar gas da kamfanin na NNPC ke yi a aikin hako albarkatun mai a yankunan da aka saba kan iyakoki, tare da kebe kaso uku cikin 100 na kudadden gudanar da ayyukan kamfanonin mai ga raya yankunan da ake hakar albarkatun mai a cikin su.
A wani bangare, shugaban kwamitin hadin gwiwar majalisun 2, Sabo Muhammed Nakudu, ya bayyana cewa zartar da kudirin PIB zuwa doka zai taimaka wajen karfafawa kamfanin NNPC a massayin mai zaman kansa, yin aiki yadda ya kamata kuma a bayyane cikin gaskiya da adalci.
Idan ana iya tunawa dai, a shekarar 2008 ne aka sake gabatar da kudirin PIB ga majalisar dattawa lamarin da ya yi ta fuskantar matsalolin koma baya a duk lokacin da aka yi magana a majalisun dokokin Najeriya.
Ko a majalisa ta 8, kiris ya rage yan majalisun su kai ga amincewa da zartarwa zuwa doka, amma aka sami gagarumin koma baya da cece-kuce kan sa.
Kudirin PIP dai ya kunshi bangarori biyar da suka hada da shugabanci da hukumomi, bangaren gudanarwa, raya yankunan da ake hako mai, tsarin tafiyar da cinikin mai da kudi, da kuma sauran wasu muhimman sharuda daban-daban da suka kunshi sassa 319 da jadawalin 8.
Majalisar dattawa dai ta amince da sharadi na 53 na kudurin da ya ba ministan albarkatun man fetur ikon mayar da kamfani man fetur na Najeriya wato NNPC a matsayin wani kamfanin mai hannun jari wato 'Limited', bayan watanni shida da fara aikin dokar ta PIB.
Haka kuma, wannan sashin dokar na 53 ya umarci ministan albarkatun man fetur da ya tuntubi ministar kudi domin tantance adadi da kuma darajar hannayen jarin da za'a ba masu zuba jari, wanda shi ne zai zama mafi yawan kason hannun jari na farko na kamafanin NNPC Limited da dai sauran su.
Kafin cimma nasarar amincewa da kudurin PIB ya zama doka, an sami rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan majalisar dattawan kan kaso mafi dacewa na ribar da za’a rika ba yankunan da ake hako mai a cikin su.
A cikin kudirin dokar da gwamnatin Najeriya ta aikewa majalisun biyu a shekarar da ta gabata, fadar shugaba Buhari ta gabatar da batun ba yankunan da ake aikin hako mai kaso 2 da digo 5 cikin 100 na ribar da za’a rika samu, lamarin da shugabannin yankunan da ake hakar mai a ciki suka ki amincewa da shi a yayin gabatar da kudirin a taron tattaunawar watan Fabrairu.
Amma kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa wanda ya yi aiki a kan kudirin ya ba da shawarar kaso 5 cikin 100 kafin daga baya aka cimma wannan matsaya.