Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole A Bar ‘Yan Kasuwa Su Kayyade Farashin Litar Man Fetur -NNPC


Hedikwatar NNPC
Hedikwatar NNPC

Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC, Mele Kyari, ya bayyana cewa, kamfanin ba zai iya ci gaba da daukar nauyin biyan tallafin man fetur da ya ke yi don saukakawa ‘yan kasa farashin kowacce litar mai ba.

Shugaban Kamfanin NNPC, Mal. Mele Kyari ne ya bayyana hakan a yayin taron mako-mako na ministocin Najeriya a fadar Aso Rock da ke babban birnin tarayyar Najeriya.

Ya ce kamafanin na NNPC yana biyan tallafin man tsakani naira biliyan 100 zuwa 120 a duk wata, ya na mai cewa, dole ne a bar ‘yan kasuwa su kayyade farashin man fetur a kasar.

Mal. Mele ya koka game da nauyin da aka dorawa kamfanin NNPC ta hanyar biyan tallafin na man fetur din, yana mai cewa, ko-ba-dade ko-ba-jima, ‘yan Najeriya za su biya ainihin farashin kowacce litar man fetur.

Malam Mele Kyari
Malam Mele Kyari

A halin yanzu dai, ana sayar da kowacce litar man fetur kasa da farashin shigowa da man cikin kasar lamarin da ya sa kamafanin na NNPC daukar nauyin cika gibin ainihin farashin, duk da yake Mele Kyari, ya gujewa bayyana adadin kudadden da NNPC ke biya na gibi a matsayin tallafi.

Ya jadada cewa kamafanin NNPC na biyan kudin ne don ci gaba da sayar da tattacen man fetur a farashin da ake sayen kowacce lita a matakin da yake a yanzu.

Mele Kyari dai ba ba da takamaiman ranar da kamfanin NNPC zai daina biyan tallafin man fetur ba a lokacin da manema labarai suka ka tambaye shi.

A wani bangare kuma, karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, ya bayyana cewa, daga nan zuwa watan Afrilu, za a zartar da kudirin masana'antun man fetur wato PIB dake gaban majalisar dokokin kasar a halin yanzu.

Ya ce kuma alamu na nuni da cewa ba za a fuskanci koma baya ba a aikin zartar da kudirin zuwa doka ba, duba da yadda shugabannin majalisun kasar ke aiki tukuru.

Timipre Sylva ya jadada muhimmancin Najeriya ta karkatar da akalar tattalin arzikin ta daga dogaro da man fetur zuwa ga iskar gas, yana mai kara da cewa, idan aka zartar da kudirin masana'antun man fetur wato PIB da ya dauki tsawon shekaru 20, zai iya janyo dimbin masu zuba jari zuwa ga bangaren iskar gas.

Dangane da batun samun matatun mai masu aiki yadda ya kamata, Timipre Sylva, ya soki lamirin tsohon dan majalisar dattawa Dino Melaye a kan furucinsa kan gaggarumin gyarar matatar man fetur ta Fatakwal da gwamnatin ta amince a yi akan kudi dala bilyan 1 da rabi.

Ministan ya ce "Melaye ba kwararre ba ne a fannin matattun mai kuma bai kamata ya tsoma baki a kan lamarin da bai da kwarewa a kai ba."

A cewar Timipre Sylva, gwamnatin tarayyar Najeriya za ta ci gaba da jajircewa kan cıka alkawarin da ta dauka na samar wa ‘yan kasar matatar mai mai aiki a kan lokaci.

XS
SM
MD
LG