Kamfanin man fetur na NNPC a Najeriya ya jaddada matsayarsa ta cewa ba zai kara kudin litar man fetur a watan Maris ba.
‘Yan Najeriya sun yi ta rige-rigen sayen man bayan da hukumar da ke kayyade farashi ta PPPRA, ta wallafa wasu alkaluma da ke nuna cewa za a kara kudin man zuwa naira 212.
Karin bayani akan: IPMAN, Malam Mele Kyari, PPPRA, NNPC, Nigeria, da Najeriya.
Sai dai a ranar Juma’a kamfanin na NNPC ya fito ya fayyace cewa babu wani shiri na kara kudin man a wannan wata.
“Kamfanin NNPC na nan akan sanarwar da ya fitar a ranar 1 ga watan Maris cewa, ba za a kara kudin mai ba.” Shugaban yada labaran kamfanin Kennie Obateru ya fadawa manema labarai a ranar Juma’a a Abuja.
“Saboda haka, babu amfanin a yi ta rige-rigen sayen man, kuma ina mai kara tabbatar muku da cewa, muna nan akan bakarmu.” Obateru ya ce.
Tuni dai hukumar ta PPPRA ta goge wadannan bayanai a shafinta.
Ita ma kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN a Najeriyar ta musanta karin kudin daga naira 163 zuwa 212.
Karin farashin kudin mai a Najeriya ba sabon abu ba ne, inda a lokuta da dama ya kan zo ba tare da mutane sun yi tsammani ba.
Najeriya ta jima tana kashe biliyoyin kudade wajen biyan tallafin man da ake shiga da shi kasar, lamarin da ke yawan janyo ka-ce-na-ce.