Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Naira Tiriliyan 33


Naira
Naira

Rahoton hukumar bincike da kididdiga ta Najeriya, ya bayyana cewa adadin bashin da ake bin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin kasar ya kai naira tiriliyan 33.11 ya zuwa 31 ga watan Maris.

A cikin rahoton da fitar jiya Alhamis dangane da “Basukan cikin gida da na waje da ake bin Najeriya a rubu’in farko na shekarar 2021”, hukumar bincike da kididdiga ta Najeriya (National Bureau of Statistics) ta bayyana cewa basukan da ake bin gwamnatocin daga wajen kasar ya kama naira tiriliyan 12.47, wato kashi 37.6 cikin dari kenan.

Basukan cikin gida ko a cewar rahoton, sun kai naira tiriliyan 20.64, wanda ya ba da kashi 62.33 cikin dari na adadin basukan.

Rahoton ya ci gaba da cewa bashin da ake bin gwamnatin tarayya na cikin gida kadai ya kai naira tiriliyan 16.51, yayin da gwamnatocin jihohi kuma suke da naira tiriliyan 4.12 na basukan cikin gida.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Masana da masu baki a Najeriyar dai na ci gaba da bayyana damuwa da yadda adadin basukan da gwamnatoci ke ci yake dada karuwa, duk kuwa da ikirarin habakar tattalin arziki da suke yi.

Ko a makon jiya ma, hukumar nan ta hada-hadar kudade wato “Nairametrics”, ta ba da rahoton cewa hukumar kula da basuka ta Najeriya ta ce basuka da ake bin kasar sun karu da naira biliyan 191 a farkon rubu’in wannan shekara, wanda ya ba da adadin naira tiriliyan 32.9 a ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2020, zuwa tiriliyan 33.1 ya zuwa karshen watan Maris na shekarar 2021.

To sai dai a nashi ra’ayin, shugaban majalisar daddatawan kasar Ahmad Lawan, ya ce Najeriya za ta ci gaba da ciyo bashi domin aiwatar da ayukan ci gaban jama’a, saboda kasar na fama da karancin kudi a halin yanzu.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan (Facebook/ Nigerian Senate)
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan (Facebook/ Nigerian Senate)

A lokacin wata hira da manema labarai jim kadan bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a jiya Alhamis, Lawan ya ce a halin da ake ciki Najeriya na cikin talauci, don haka ba ta da wani zabi illa ta ciwo bashi domin samar da kudade ga bangarorin ta na tattalin arziki.

Ya kara da cewa majalisar dokoki ba za ta dage akan hana bukatun gwamnati na ciwo bashi ba, to amma ya ce tana sa ido domin tabbatar da yin kyakkyawan amfani da basukan.

XS
SM
MD
LG