Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NNPC Ya Ba Da Kwangilar Dala Biliyan 1.5 Don Gyaran Matatar Mai Ta Fatakwal


Shugaban NNPC Mele Kyari (tsakiya) a lokacin da aka rattaba hannun a kwantiragin
Shugaban NNPC Mele Kyari (tsakiya) a lokacin da aka rattaba hannun a kwantiragin

Kamfanin mai na Najeriya NNPC, ya rattaba hannu a kwangilar dala biliyan 1.5 don gyaran matatar mai da ke garin Fatakwal a jihar Rivers.

Kamfanin na NNPC ya rattaba hannun ne da kamfanin Maire Tecnimont SpA na kasar Italiya karkashin jagorancin kamfanin Malam Mele Kyari.

“An rattaba hannun ne a gaban ma’aikatan kamfanin na NNPC da sauran masu ruwa da tsaki da suka hada da hukumar tabbatar da adalci a harkar hakar mai ta NEITI, kungiyar PENGASSAN da dai sauransu.” Wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka Halima Abdulra’uf da ta halarci zaman ta ruwaito daga Abuja.

Batun yin garanbawul ga matatar man ta Fatakwal, ya janyo suka daga ‘yan Najeriya ciki har da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar.

A ‘yan kwanakin da suka gabata ne, yayin wani zama da ta yi, majalisar zartarwar kasar ta amince da a kashe wadannan makudan kudade wajen gyaran matatar man.

Malam Mele Kyari
Malam Mele Kyari

Tun daga lokacin, jama’a da dama suka yi ta sukar matakin,

“Akwai lauje cikin nadi a yunkuri kashe dala biliyan 1.5 don gyaran matatar mai ta Fatakwal.” Atiku Abubakar ya rubuta a shafinsa na Twitter a tsakiyar watan Maris.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya kara da cewa, “tattalin arzikinmu ba zai ci gaba a haka ba, idan muka dore da zuba kudade akan abin da ba ya haifar mana da sakamako mai kyau.”

Sai dai Kamfanin NNPC, ya fito ya yi karin haske kan abin da ya kira “gurguwar fahimta” da mutane suka yi wa kudaden da za a kashe, inda ya ce kudaden na gyara daukacin matatar ne ba wai na kananan gyararraki ba ne.

Ita dai matatar man ta Fatakwal, kan samar da gangar mai dubu 210 kowace rana.

Najeriya dai kan aika da danyen manta zuwa kasashen waje ne inda akan tace shi a maido da shi kasar akan kudaden masu yawa.

XS
SM
MD
LG