Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matukan Jirgin Sama Sun Ba Hammata Iska A Sararin Subuhana


Mahukunta harkokin jiragen saman kasar India sun dakatar da lasisin tuka jirgin sama na wadansu matuka jirgin sama guda biyu, bisa laifin dambe da sukayi a cikin jirgi a lokacin da yake sararin samaniya, a farkon shekarar nan ta 2018.

Babban daraktan harkokin jiragen saman ya gudanar da bincike akan aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewar halinsu ya saka rayuwar jama'a da dama cikin hadari, hakan yasa aka zartar da hukuncin dakatar da lasisin su.

Kamfanin jirgin saman Jet Airways ya kori matukan jirgin sama ‘yan asalin kasar India, babban matukin namiji da mataimakiyar sa, bayan da hukumar harkokin jiragen sama ta dakatar dasu daga tukin jirigin sama har na tsawon shekaru 5.

Lamarin ya auku ne a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2018, a cikin jirgin sama dake hanyar sa ta zuwa Munbai daga Birnin Landon wanda zai dauki kimanin awoyi 9, a sararin samaniyar Iran zuwa Pakistan, inda babban matukin ya mari mataimakiyar tasa a cikin dakin tukin jirgin, jirgin dai na dauke da mutane 322.

A cewar shaidu, babban matukin ya mari mataimakiyar tasa ne biyo bayan wata rigima da su kayi, daga bisani ta bar dakin tukin jirgin sai bayan da wani babban matukin ya saka baki sannan ta koma kan aiki.

Kamfanin jirgin saman Jet Airways ya ayyana rigimar da ma’aikatan suka yi a matsayin rashin fahimtar juna, kuma sun daidaita a cikin lumana.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG