Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'ar Kasar Afrika Ta Kudu Zata Fara Koyar Da Darussan Maita


Ministan ilimin kasar Afrika ta Kudu Mr. Blade Nzimande, ya bayyana kudurin gwamnatin kasar na saka darussan karatun Maita a cikin tsarin manhajar karatun kasar.

Za’a fara koyar da karatun maita, yadda mutane zasu fara tashi sama ciki dare kamar yadda mayu ke yi, ya bayyana cewar za’a saka tsarin cikin manhajar koya karatu ta kasar a wannan shekarar 2018.

Ministan ya bayyana hakane a lokacin ganawarsa da wakilan dalibai na kasar, ministan ya bayyana wannan matakin da cigaba da daukar hankalin ‘yan kasar, inda ya bukaci jami’o’in kasar da su fara tunanin koyar da darussan maita a azuzuwan su.

Ministan ya kara da cewa, “Zamu koyi abubuwa da dama a cikin wannan karatun, domin kuwa zamu koyi yadda mayu ke tashi sama a cikin kwando, idan kuwa mutane suka iya tashi cikin Kwando, lallai hakan zai saukaka matsalar cinkoso a kan tituna, domin kuwa mutane zasu dinga tashi cikin Kwanduna batare da matsar tafiya a hankali ba” haka kuma ba sai kasar ta rika sawo man futur daga wasu kasashe ba.

Ministan ya bukaci Mayu a baki dayan kasar da su zo don su gana da shi, kuma idan suna bukatar aiki za’a gwadasu don a basu aikin koyar da ilimin mayu a jami’o’in. Ya kuma bukaci duk Mayun da suke nahiyar Afrika da suzo kasar za’a basu takardun zama ‘yan kasar na dindindin.

Daga karshe ya kara da cewar, ya zanta da ministan cikin gida don amincewa da tsarin ba Mayu izinin zama ‘yan kasa wanda ya amince da hakan, za’a cigaba da karbar takardun shiga daga nan har zuwa ranar 30 ga watan Satumba, daga nan sai a fara tantance kwararrun mayu don basu aikin koyar da daliban.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG