Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amazon Ya Bude Shagon Sayar Da Kaya Mara Ma'aikata


Babu mai karbar kudi, babu bin layi, babu wajen biyan kudi, cigaban kimiyya a karni na 21, ya kawo zamanin babu mai tsaron shago! Shahararren kamfanin hada-hadar kasuwancin yanar gizo na Amazon, ya kaddamar da sabon tsarin kasuwancin tsakanin mai saye da na'ura..

Kamfanin na Amazon ya bude sabon shagon da ake sayarda kayayyaki kamar su madara, dankali, biskit, lemo, da dai makamantansu, abu kawai da mutun ke bukata shine ya shiga shagon don daukar abin da yake bukatar saye, idan mutun ya kammala, sai ya biya da wayar sa ba tare da Magana da kowaba.

A duk lokacin da mutun ya dauki abu daga saman kanta kai tsaye na’ura zata nuna mutun ya dauki abu kaza da kuma kudin sa, idan kuma mutun ya maida abin bashi da bukata, take na’ura zata bayyana cewar ka ajiye abin da ba a bukata.

Sabon tsarin dai zai ba mutane damar gabatar da sayayya kamar yadda mutane ke yin sayayyar su a yanar gizo, amma mutun na cikin shago don zabe da biyan kudi ba tare da wata mu’amala da mutunba, duk cinikin mutun zai kasance tsakaninsa ne da na’ura.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG