Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Zai Fara Daukar Labarai Masu Matukar Muhimanci


Kamfanin Facebook ya bayyana cewar zai fara tantance gidajen jaridu, da daukar gidajen da sukafi shahara wajen bayyayana labarai masu tushe. Wannan yunkurin ya biyo bayan kokarin kamfanin na yaki da labarai da basu da tushe.

Kamfanin ya bayyana cewar zai nemi ra’ayoyin mutane da suke mu’amala da shafin wanda suke da mutane sama da billiyan biyu a fadin duniya.

Za’a baiwa mutane damar bayyana ra’ayoyinsu akan gidajen jaridu da suke fadin gaskiya komi dacin ta, kana gidajen jaridun masu fadar labarai masu tushe.

Duk gidajen jaridu da aka samesu da bayyana labarai marasa tushe, kamfanin na Facebook ya dau alwashin rufe shafukan gidajen jaridar a shafin sa.

Wannan wata hanya ce da za’a magance labarai marasa tushe, da wasu kanyi amfani da shafin wajen yadasu. A cewar shugaban kamfanin Mark, akawai labarai da basu da tushe kuma suna yaduwa a shafin na facebook.

Don haka lokaci yayi da kamfanin zai fara tankade da rai-raya na tushen labarai.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG