Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Gwajin Farko Wajen Samar Da Wutan Lantarki A Duniyar Wata


Wasu gwaje-gwaje da aka gudanar a jihar Nevada daKe Amurka kan wata fasahar samar da wutan lantarki ta hanyar amfani da ilimin Nukiliya, wacce aka kera ta domin samun dogon wa’adin zama cikin duniyar wata, da nufin gudanar da bincike sun yi nasara, har zasu fara aiki a watan Maris.

Hukumara kula da bincken ta 'Natioanl Aeronautics and Space Administration tare da ma’aikatar hukumar makamshi ta Amurka, sun bayyana cigaban da aka samu.

An fara gwajin tun a watan Nowamba, a ma’aikatar makamashi dake jihar ta Nevada, da neman hanyoyin da za’a inganta tsarin samar da wuta a cikin jirgin kumbo afolo da ma’aikan sama jannati zasu ci gajiya.

Tun a shekarun 1969 zuwa 1972 aka fara samar da tsarin samar da wuta ga ‘yan sama jannati, amma a wannan karon an samar da sabuwar hanya don inganta wutar domin jin dadi da walwala na ma’aikatan hukumar ta NASA.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG