Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmar Farko Najat 'Yar-Takarar Kujerar Majalisar Dokoki


Najat Driouech
Najat Driouech

Abun nada bacin rai duk lokacin da ka bude akwatin talabijin naka, ba zaka taba ganin bakin mutun ba ko balarabe, a cewar matashiya Najat Driouech, ‘yar takarar kujerar majalisar dokokin jihar Catalonia, a kasar Spain, Al-Andalus.

Ta kasance mace ta farko da ta samu kyaututuka har ta samu damar zuwa jami’a, kuma ta bada kyakyawar gudunmawa wajen ciyar da garin nasu gaba, Najat, tace “Ba ina son shiga majalisa bane don na zama mace ta farko musulma da ta zama ‘yar-majalisa.”

Sai dan inaso na kawo canji a cikin al’ummar mu, bana kuma fatar ‘ya’yana suyi irin wahalar da iyaye na su kayi, koma a ce irin wadda nayi. Iyayen ta sun fito daga kasar Morocco, a lokacin da take ‘yar shekaru 9 a shekarar 1990.

Baki daya rayuwar ta tayi su ne a wannan karamar hukumar, kudurin ta ya biyo bayan yunkurin gwamnatin kasar ta Catalan, da suka bayyanar da samun ‘yancin kai daga kasar Span, wanda hakan ya zama karya doka.

Matashiyar ta bayyanar da kudurin ta na ganin ta kawo cudanya a yanki, da ba kowa hakkin shi batare da wariyar launin fata, ko banbancin addini da na akida ba.

Najat, tace lallai wannan matakin nata yazo a cikin mawuyacin hali, amma tabbas akwai bukatar wayar da kan jama’ar yankin, don ba kowa damar nuna bajintar shi, musamman mata.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG