Magagin Bacci kan iya zama wani hatsari ga rayuwar bil’Adama, a cewar wani masanin kwakwalwar bil'Adam, Dr. Guy Leschziner, ya ce sau da yawa akan samu mutane da ke da nauyin bacci, har su kanyi wasu abubuwa duk a cikin baccin.
Hakan yakan zo da hadari a wasu lokuttan, Jackie, wata mata dake da nauyin bacci sosai, ‘yan kwanaki kadan bayan ta bar kasarta ta haihuwa Canada, zuwa kasar Ingila.
A cikin irin magagin baccin ta, tayi tukin mashin da mota, duk batare da ta san abun da tayi ba. Daya daga cikin mutanen da take zaune da su, sun lura da yadda take fita cikin tsakka dare, tana sanye da hular kwano.
Da gari ya waye an tambaye ta ko ina take zuwa tsakar dare? Takan kwashe mintoci kamar 20, sai ta amsa da cewar bata zuwa ko ina, an shaida mata yadda take fita cikin tsakiyar dare, ta bayyana cewar bata iya tuna komai ke faruwa da ita a cikin dare.
Bayan ‘yan kwanaki kadan ta sake fita tsakiyar dare, inda ta fita da mota, a dai-dai lokacin da aka kaita wajen likita, ya iya gano cewar tana dauke da wata cuta mai sa nauyin bacci. Likitan ya iya tabbatar da cewar duk abubuwan da matar tayi lallai tayi su ne cikin nauyin bacci.
Ta bayyanar da cewar, lokacin da take karama tana minshari mai kara, wanda hakan yasa ‘yan uwanta basa son kwanciya kusa da ita, don karar minsharin baccin ta yana basu tsoro.
Tana iya tuna labarin da iyayen ta suka bata na yadda take tasowa cikin tsakiyar dare, tana yawo ko yin wasu abubuwa batare da tasan abun da ta keyi ba. Sai da safe su bata labarin abun da tayi, ta amsa cewar wannan ba wani bakon abu bane a gare ta, domin kuwa ta dade tare da wannan matsalar.
Facebook Forum