Halima Ibrahim Idris, wata matar auren ce wacce ta jajirce wajen neman ilimi domin ta cimma burinta na rayuwa.
Tace ta koma makarantar boko bayan anyi mata aure tana da shekaru 13, a duniya amma hakkan bai hanata cigaba da neman ilimi ba domin zama Nas mai aikin asibit domin shine burinta a rayuwa.
Bayan kammala karatun horo a matsayin mai aikin asibiti sai ta sami gurbin aiki a asibitin koyarwa na Mahaukata, inda ta ce ta fara aiki a can tare da nuna jajircewa da kwazona sai wani ma’aikaci ya bata shawarar komawa makaranta don inganta karatunta.
Halima tace bayan komawarta inda ta samu shiga makarantar koyon fasaha jinya, ta cigaba da wasu kwasa-kwasai don cigaba wajen inganta karatuna na Nas watau mai kula da marasa lafiya.
Tace ta fuskanci ‘yar matsala kasancewarta ga ta yarinya da aure ga kuma karatu, a yayin da take karatun tana kuma sana’a domin tallafawa karatunta.
Ta ce a wancan lokaci idan suka tashi daga makaranta takan je makarantar koyon sana’oin dogaro da kai inda take zuwa koyon dinkin.
Facebook Forum