Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Kaina Na Koyi Dabarun Inganta Sana'ar Waka A Yanar Gizo - Nexus


Nexus
Nexus

Daga lokacin da na yi hira da dandalinVoa zuwa yanzu na kara samun damar aiki da manyan mawaka tare da samun wasu Karin kyaututtuka a bangaren sound engineering, sannan na sake samun lambar yabo ta best producer a kyaututtukan da ake badawa na best producers of the year na fina-finan Kannywood bayan editing din waka da nake yi inji Nexus Pitch wanda aka fi sani da Nexus.

Nexus, ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA, inda ya bayyana mata cewa a yanzu yana tace fina-finai tare da cire iska da wasu sautuka da ba’a so yadda zai yi daidai da fina-finan da ake sawa a cinema, ya ce ya sami Karin ilimin yadda ake gyara sauti ne a yanar gizo inda yake karatu don ya inganta harkarsa.

Ya ce yanzu ya kai ga har manyan mawaka daga Lagos, na zuwa wajensa domin suyi waka tare da cewar a ‘yan kwanakin nan ma ya sami bakuncin mawaki Kenny Wonders, inda zasu yi waka a tare.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:51 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG