Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Twitter Ya Dau Alwashin Kawo Karshen Kiyayya A Duniya


A jiya Litinin kamfanin Twitter, ya fitar da sanarwar sabon tsari, da zai rika kula da ire-iren hotuna da mutane ke sakawa a shafukan su. Da duk wani hoto dake dauke da wasu kalamai na kiyayya, baza a sake barin mutane na saka irin su ba.

Wannan na daya daga cikin matakan da kamfanin zai dauka, don kawo karshen kiyayya na wariyar launin fata, jinsi, kabila, ko addini, da kan kawo aikin ta’addanci a cikin al’umma.

Kamfanin ya kara da cewar, zai kulle duk wani shafi da ake amfani da shi, wajen ruruta wutar kiyayya, ko nuna wasu akidoji marasa kyau. Kamfanin da aka kirkira tun a shekarar 2016, yana takama da cewar, shine shafi daya da mutane kan iya bayyana ra’ayoyin su, batare da tsangwamaba. Kuma yana kokari wajen kawo sulhu a tsakanin ma’abota amfani da kafar.

Karuwar kungiyoyi masu karfafa akidar wariyar launin fata, a kasar Amurka sun kawo sauyi kwarai a duniyar kimiyya da fasaha, kamfanin na cigaba da yaki da munanan halaye, da muzgunawa mata, da cin zarafin yara, da akanyi a kafofin yanar gizo.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG