Akwai kalubalen rashin fahimta daga wajen al’umma mussamam yadda jarumai ke fitowa a wasu fina-finai sai jama’a su dauka irin halaye ko dabi’un Kenan inji Ghali Ibrahim ‘yan doya wanda aka fi sani da Ghali Bahi.
Matashin ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakiliyar DandalinVOA, inda ya bayyana cewa ya fara fim ne tun yana dan yaro inda suke fim na Islamiyya wanda dama can yana sha’awar yin fim tun yana karami
Bahi, ya ce ya fara fim ne da ‘yan unguwa inda suka rubuta fim a kan damfara tare da jarumi daya wanda shine sananne a wancan lokaci.
Ya ce suna isar da sakonni ga al’umma ta hanyar amfani da wasu halaye na wasu mutane domin nusar da al’umma illa ko alfanun aikata wata dabi’a da sauransu. Bahi, ya ce har yanzu mutane basa tantance cewar halayyar jarumi a fim fim ba halaiyar sa ta gaskiya ba ce.
Facebook Forum