Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakan Amurka a kasar Afghanistan


Ganawar Shugaba Trump da 'yammatan Chibok
Ganawar Shugaba Trump da 'yammatan Chibok

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana rawar da Amurkja zata dauka a kasar Afghanistan kumawannan yana cikin jawabin da zai gabatar a daren littinbi.

Shugaban Amurka Donald Trump zai zayyana jadawalin matakan da Amurka za ta dauka a Afghanistan a wani jawabin da zai gabatar da daren yau dinnan Litini.

Trump zai "bayyana halin da ake cikin game alkiblar da Amurka za ta fuskanta a ayyukan soji da ta ke yi a Afghanistan da kuma Kudancin Asiya" a wani jawabin da zai yi da dare daga sansanin sojin Fort Myer dake Kudu maso yammacin babban birnin Amurka, a cewar wata sanarwar da Fadar White House ta gabatar.

Jiya Lahadi, Sakataren Tsaron Amurka James Mattis ya ce Trump ya yanke shawara kan sabuwar dabarar da za a yi amfani da ita a Afghanistan, to amma bai yi wani cikakken bayani ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG