Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Amurka Ta Ke Fargabar Ficewa Daga Afghanistan


Dakarun Amurka suna sauraren jawabin shugaba Donald Trump yayin da yake magana akan matakin da yake so ya dauka a Afghanistan
a sansanin soji na Fort Myer da ke jihar Virginia, Ranar 21 ga watan Agusta 2017.
Dakarun Amurka suna sauraren jawabin shugaba Donald Trump yayin da yake magana akan matakin da yake so ya dauka a Afghanistan a sansanin soji na Fort Myer da ke jihar Virginia, Ranar 21 ga watan Agusta 2017.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa 'yan kasar jawabi kan dabarun yadda zai tunkari yakin Afghanistan yayin da Amurkawan suka fara dasa alamar tambayar shin ko kwalliya ta biya kudin sabulu kuwa?

Amurkawa sun fara nuna damuwarsu akan shirin fidda sojojinsu a Afghanistan, daga yakin da kasar ta kwashe lokaci mai tsawo tana yi da ‘yan ta'adda, ba tare da samun ko wacce irin nasara ba.

Sai dai ficewar nata zai iya haifar da gibi ga ‘yan ta'addan kamar yadda shugaban na Amurka Donald Trump ya fada jiya littini, a lokacin da ya yi wa Amurkawa jawabi akan sabon shirinsa ko kuma dabarar da yake so ya kaddamar game da kasar ta Afghanistan.

"Ba shakka ficewar gaggawa za ta samar da wani gibi na musammam ga ‘yan ta'adda, ciki har da kungiyoyin ISIS da na Alqaeda, wanda wannan zai sa su fadi warwas kamar abinda ya faru a ranar 11 ga watan Satumba, kuma kamar yadda muka sani a shekarar 2011, Amurka ta yi gaggawar tare da kuskuren janyewa daga kasar Iraqi."

Trump ya yi wadannan kalamai ne yayin da yake jawabi ga dakarun Amurka kan matakin da yake so ya dauka kan yakin na Afghnistan a sansanin Fort Myer dake jihar Virginia.

Sai dai kuma, shugaban na Amurka, ya yi shekaru yana sukan lamirin gwamnatin kasar ta Amurka game da rawar da Amurkan ke takawa a kasar ta Afghanistan, yana cewa ba a kome sai barnar kudi da lokaci.

Akalla sokojin Amurka 8,400 ke jibge a Afghanistan, ko da yake, mafi aksarinsu, sukan baiwa dakarun kasar shawara ne, duk da cewa akwai wasu daga cikinsu da ke taimakawa wajen kai wa 'yan Taliban farmaki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG