Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan kasar Hong Kong Sun Gudanar Da Zanga-Zanga


Matasa 'Yan Afirka Mazauna Amurka Sun Gudanar Da Zanga Zanga
Matasa 'Yan Afirka Mazauna Amurka Sun Gudanar Da Zanga Zanga

'Yan kasar Hong KOng sunyi bore akan hukuncin da gwamnatin kasar ta yanke aka wasu mutane 3 masu rajin kare demokaradiyya.An yanke musu hukunci dauri ko biyo bayan rawart da suka taka na nuna kyamar gwamnati tun a shekarar 2014

Dubun dubatan jama'a sun yi gangami a Hong Kong jiya Lahadi a wata zanga-zangar nuna rashin amincewa da hukuncin da aka yanke ma wasu 'yan rajin demokaradiyya su uku, wadanda su ka jagoranci wata kungiyar gwagwarmaya ta 2014.

Hukuncin da aka yanke masu din ya gamu da fushin kungiyoyin kare 'yancin dan adam da sauran 'yan gwagwarmaya, wadanda su ka hada kai da farar hula jiya Lahadi daga gundumar Wan Chai zuwa kotun daukaka kara don yin zanga-zangar nuna rashin amincewa da hukuncin daurin.

Wadanda su ka shirya gangamin ba su bayar da kiyasin wadanda su ka hallara ba, to amma 'yan sanda sun ce mutane wajen 22,000 su ka halarcin gangamin, wanda ya zama gangami mafi girma da Hong Kong ta taba gani tun bayan lokacin da aka kafa kungiyar.

'Yan kasar Hong kong

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG