Wani sabon rahoto na nuni da cewar an samu karin yawan mata dake mutuwa sanadiyar shaye-shaye a fadin duniya. Wanda mata kalilan ne kan samu kulawa da ta dace, idan aka hada da adadin maza da kan samu kulawa a fagen shaye-shaye.
Rahoton karshen shekara na hukumar kasa-da-kasa don yaki da kwayoyin Narcotic, sun bayyanar da cewar gwamnatoci basu kulawa da wannan bangaren yadda ya kamata, musamman idan akayi la’akari da yadda yawan mata ke karuwa a wajen shaye-shaye.
Hukumar dai na bibiya ga tsarin majalisar dinkin duniya, wajen magance matsalolin shaye-shaye, wanda suke ganin cewar ana kyale mata da wannan matsalar, ba’a basu kulawa ta musamman.
A ta bakin shugaban kungiyar Mr. Werner Sipp, kashi daya bisa uku na mashaya a fadin duniya mata ne! Amma kaso daya bisa biyar ne kawai suke samun kulawa ta musamman. Hakan na nuni da cewar ana nuna wariya a tsakanin mata da maza. Akan horas da mata fiye da irin horon da akanyi ma maza mashaya.