Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manhajar Zakulo Labaran Bogi A Shafin Facebook Ta Fara Aiki


Facebook ya kaddamar da wata sabuwar manhaja da yace zata taimaka wajen gano labaran bogi a shafinsa.

Ita dai wannan mahaja za ta rika taimakawa wajen zakulo labaran karya da aka kafe, wadanda kuma aka bayyanasu a matsayin na bogi da taimakon abokan hadin gwiwar Facebook da suka hada da Snopes, da politifact, da kuma shafin factcheck.org.

Tun watan Disambar bara dai Facebook, ya bayyana cewa zai kaddamar da wannan manhaja, amma sai yanzu ta fara aiki.

Idan wani daga cikin masu amfani da shafin Facebook wadanda yawansu ya kai Biliyan 1.86 ya bada rahotan wani labarin boge, kamfani zai aika da labarin ga abokan hadin gwiwarsa domin su tantance gaskayar labarin. Idan kuma aka samu tabbacin labarin kanzon kurege ne, to za a yiwa labarin shaida a kuma kafe bayanin da yasa ya zama labarin karya.

Facebook ba zai cire labarin da aka tabbatar da rashin sahihancinsa ba, kuma mutane zasu iya aikawa abokansu, sai dai za a gargadi mai aikawar cewa labarin bana gaskiya bane.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:10 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG