A karni na ashirin da daya 21 da muke ciki, wani babban abun mamaki, da ya faru da wani mutun. Ga ma’abota kallon fina-finai, ‘yan shekarun baya anyi wani fim mai suna “Tarzan” wanda ya bayyanar da rayuwar wani mutun a cikin daji, wanda yake koyi da rayuwar dabbobi.
A yankin wani tsibiri na “Quang Ngai” a kasar Vietnam, wani mutum yayi gudun tsira cikin kungurmin daji, tun lokacin yakin duniya na Vietnam, a shekarar 1972. Bai sake dawowa cikin jama’a ba, ya kwashe tsawon rayuwar shi, cikin daji da rayuwa irin ta namun daji.
Wasu jerin manazarta da suka shiga cikin dajin, da babu mahaluki da ya taba shiga ya fito, sai gashi sun tsinci wannan mutumin, sunyi kokarin yin magana da shi bai san abun da suke cewa. Bayan gudanar da bincike sun iya gano cewar, ya kwashe tsawon sama da shekaru arba’in zuwa arba’in da hudu, 40-44 a cikin dokar daji shi kadai.
Allah ya bashi basira, wanda ya gina gidan kara, kuma yana cin abinci daga farauta da ya keyi na namun daji. Wata baiwa da yake da wanda yake iya kama tsuntsu, ko bera da sauri fiye da yadda mutun zai shiga shafi a yanar gizo don binciken wani abu, sabo da tsabar sauri.
Baki daya rayuwar shi a cikin dajin yayi ta, wanda bai san mutane ba, bai iya rayuwa ta mutane ba, yana amfani da ganyen itace don suturta jikin shi. Bai iya magana ba, sai dai kukan tsuntaye, da na sauran namun daji. Yanzu haka dai yana tare da hukumomi don samun magartaciyyar rayuwa.