WASHINGTON D.C —
A yayin da ake bikin ranar mata ta duniya, a jihar kano wakiliyar wayar da kan al'umma ta karrama hukumar Tarauni karkashin asusun tallafawa yara ta majalisar dinkin duniya Malama Jamila Suleman Gezawa, ta shirya wani taron gangamin wayar da kan mata kan 'yancin basu lafiya da jaririnsu.
Daya daga cikin wadanda suka hallarci taron Malama Bilkisu Usman, ta ce taron na da muhimmanci domin kuwa a fadakar da su muhimmanci digon allurar riga kafin jararin tun daga haihuwa har na wani lokaci.
Majalisar dinkin duniya dai ta ware ranar 8 ga watan Maris na kowacce shekara a matsayin ranar tunawa da mata a fadin dunya baki daya, kuma maudu'in wannan rana na wannan shekara shine ‘Jajircewar Mata domin kawo canji ga rayuwa'.